Bolt ya yi nasara a tseren mita 100

usain bolt Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Usain Bolt

Dan tseren Jamaica na mita 100 Usain Bolt ya yi nasara a gasar Olympics ta London inda ya kammala gudun a cikin dakika 9.63 wanda hakan ya sa ya sami lambar zinariya ta gasar.

Da tseren wanda aka yi ta maganganu akan yuwuwar kare lambar tasa wanda kuma sau biyu takwaransa dan Jamaica Yohan Blake yana tsere masa a tseren fidda gwani na wadanda zasu wakilci Jamaica a Olympics, ya yiwa Yohan Blake wanda ya zo na biyu fintinkau a tseren.

Yohan Blake wanda ada ake ganin zai tserewa Bolt din ya kammala tseren a cikin dakika 9.75 ya sami lambar azurfa yayin da Justin Gatlin na Amurka yazo na uku a cikin dakika 9.79 ya sami lambar tagulla.

Wannan dai shi ne gudu mafi sauri na biyu a tarihi.

Karin bayani