Murray ya zama zakaran Olympics na Tennis

andy murray Hakkin mallakar hoto All Sport
Image caption Andy Murray

Dan wasan tennis na Burtaniya Andy Murray ya sami nasarar lambar zinariya ta wasan Olympics bayan da ya yi galaba akan Roger Federer na Switzerland a zagayen wasa uku a jere.

Murray ya lallasa Federer ne wanda shi ne zakaran duniya a wasan da ci 6-2 6-1 6-4. a abin da yake kamar ramuwar gayya ce ta yadda Federer din ya lallasa Murray din kusan wata daya da ya wuce a wasan karshe na gasar wimbledon.

Da wannan nasara yanzu Andy Murray dan shekara 25 ya zama dan Burtaniya na farko da ya sami nasarar cin lambar zinariya ta wasan tennis na 'yan wasa dai-dai maza tun bayan da Josiah Ritchie yaci lambar a 1908.

Juan Martin del Potro dan Argentina shi ne ya zamo na uku na gasar bayan da ya sami nasara akan Novak Djokovic dan Serbia da ci 7-5 6-4.

Bayan ya yi nasara akan Federer Andy Murray ya sake yin wani wasan na karshe na 'yan wasa bibbiyu tare da Laura Robinson sai dai a wannan karon sun sami lambar azurfa ce bayan da abokanan karawar tasu Victoria Azarenka da Max Mirnyi suka yi galaba akansu da ci 2-6 6-3 10-8.

Haka kuma a gasar tennis din ta mata ta 'yan wasa bibbyu Serena da Venus Williams Amurkawa 'yan gida daya sun kafa tarihi na zama na farko da suka dauki lambar zinariya ta wasan sau uku a jere.

Amurkawan sun sami nasara ne akan Andrea Hlavackova da Lucie Hradecka 'yan Jamhuriyar Czech da ci 6-4 6-4.

Karin bayani