Wani dan wasan Najeriya ya rasu a Romania

shugaban hukumar kwallon kafa ta najeriya amin maigari
Image caption shugaban hukumar kwallon kafa ta Najeriya Amin Maigari

Wani dan kwallon kafa dan Najeriya ya mutu bayan da ya fadi a fili lokacin da ake tsakar wasa a Romania.

Chinonso Ihelwere Henry ya fadi ne lokacin da kungiyarsa FC Tulcea ke wasan lig na rukuni na biyu da kungiyar Balotesti ranar Lahadi.

Kokarin da likitoci suka yi na farfado da shi ya ci tura bayanda zuciyarsa ta daina bugawa kuma numfashinsa ya dauke.

Tun a shekara ta 2010 ne dan wasan mai shekaru 21 ya ke bugawa kungiyar ta Tulcea wasa bayan da ya je kasar Romania a 2007.

Ana wasan ne a garin Baltoesti arewa da Bucharest babban birnin Romania.

Karin bayani