Da wuya Afrika ta dauki Kofin Duniya ba da kocin gida ba - Blatter

sepp blatter Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Sepp Blatter

Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya Sepp Blatter ya ce da wuya wata kasar Afrika ta dauki Kofin Duniya idan kasashen basa bada muhimmanci wajen daukar koci dan kasa da zai horar da 'yan wasansu.

Blatter yace dole ne mai horadda 'yan wasa ya kasance ya damu da 'yan wasansa ya san yanayinsu ya kuma fahimce su da kyau.

Yace ''misali ka duba Najeriya 'yan wasanta na iya kasancewa a kasashen Turai amma kocinsu dole ya fahimcesu ya lakance su sosai, ta yaya wanda ya ke daga kasar waje zai iya haka ?''

Haka kuma Blatter na ganin kasashen Afrika na fama da matsalar rashin yin shiri akan lokaci da hakan ita ma wata matsala ce a harkar wasan

kwallon kafa a nahiyar.

Shugaban FIFA din yace ''duba yadda sauran kungiyoyin kwallon kafa suke shiri da kudaden da suke kashewa da irin shirin da suke yi na shiga

gasa,amma kasashen Afrika a wasu lokutan suna daukar koci ne yayin da ya rage 'yan watanni a fara gasar cin Kofin Duniya''.

Duk da cewa babu wata kasar Afrika da ta sami nasarar zuwa gaba da matakin wasan gab da na kusa da na karshe a gasar Olympics, Blatter yayi

imanin cewa kasashen Afrika sun fi kokari a matakin wasan matasa.

Haka kuma Blatter ya nanata cewa wannan shi ne wa'adinsa na karshe na shugabancin hukumar.

Yace a lokacin da zai kammala wa'adinsa na yanzu na shekara hudu a 2015 zai zama ya yi shekaru 17 yana shugabancin hukumar, kuma a lokacin ya kai shekara 79 a duniya kuma yayi shekaru 40 yana aiki da FIFA, hakan ya ishe shi.

Karin bayani