Olympics: Kasashen Afrika na samun koma baya

Image caption Wani dan tsere daga Africa a gasar

A yayinda gasar wasannin Olympics ta shekara 2012 da ake yi a London ta shiga rana ta 10, Kawo yanzu dai kasashe fiye da 50 ne suka shiga jerin kasashen da suka samu lambobin bajinta na gasar daga na zinari zuwa na azurfa ko kuma tagulla.

Kasar China ce kuma ke kan gaba, yayinda Amurka ke take biye ma ta baya, sannan Brittaniya mai masaukin baki a matsayin ta 3 da samun lambobi fiye da 30.

To, sai dai har yanzu kasashen Afrika ba su tabuka wani abin azo a gani ba a gasar.

Kasashe irinsu Nijeriya koda lambar tagulla ba su samu ba, duk kuwa da cewar sun shiga gasar ne da tawaga marar girma da suke jin za ta taka rawar gani.

Karin bayani