Mancini ya fidda tsammanin dawowar Van Persie City

robin van persie Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Robin van Persie

Kocin kungiyar Manchester City Roberto Mancini ya ce baya tsammanin kyaftin din Arsenal Robin van Persie zai dawo kungiyarsa.

An tambayi Mancini ne akan inda suka tsaya game da dawowar dan wasan kungiyar ta su sai ya ce ''Van Persie ? A'a bana jin zai zo nan''.

Tun a watan Yuli ne Van Persie wanda Kwantiraginsa da Arsenal zai kare a kakar wasanni ta gaba yace ba zai sabunta kwantiragin ba.

Abin da ya sa Manchester City da United da kuma Juventus suka shiga neman sa amma suka kasa biyan kudin da Arsenal ta sa a kan dan wasan mai shekaru 29.

Dan wasan ya kasance cikin tawagar 'yan Arsenal da ta je Jamus domin zaman sansanin atisaye a makon nan.

Sai dai abin jira a gani yanzu shi ne ko zai buga wasan da Arsenal din zata yi da Cologne ranar Lahadi.

Duk da cewa Manchester City ta hakura akan neman dan wasan amma har yanzu Manchester United da Juventus ba su hakura ba sai dai basu kara farashin da suka saye shi ba.

Karin bayani