Arsenal na shirin bayyana sayen Carzorla

Hakkin mallakar hoto
Image caption Santi Cazorla

Kulob din Arsenal na dab da sanarwar cewa ya sayi dan wasan tsakiya na Malaga, Santi Cazorla, bayan da aka tabbatar da koshin lafiyarsa.

Carzorla ya shiga kulob din ne a lokacin da suke atisaye na gabanin kakar wasan bana a wajen horar da 'yan wasa da ke Jamus.

Dan wasan mai shekaru 27, wanda dan kasar Spain ne, zai sanya hannu a kwantiragi da kulob din na tsawon lokaci a kan fan miliyan goma sha biyar.

Matsalar karancin kudi da Malaga ke fama da ita ta sa an samu jinkiri wajen komawarsa Arsenal, sai dai ana sa ran za a sanar da komawarsa a ranar Talata.

A gefe guda kuma, Arsenal na tattaunawa domin aron dan wasan tsakiya na kulob din Real Madrid, Nuri Sahin.

Shugabannin kulob din na fatan samun wadannan 'yan wasan zai kara wa kulob din tagomashi bayan dan wasan gaba na Jamus, Lukas Podolski da kuma dan wasan tsakiya na Faransa, Olivier Giroud sun koma kulob din.

Karin bayani