‘Yan wasan Kamaru 7 sun tsere daga Olympics

dan wasan damben boksin na kamaru  yana daga cikin wadanda suka tsere Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption dan wasan damben boksin na kamaru yana daga cikin wadanda suka tsere

‘Yan tawagar wasannin Olympics guda 7 daga Kamaru sun tsere daga sansaninsu a London kamar yadda hukumomi suka tabbatar.

‘Yan wasan bakwai da suka hada da ‘yan damben boksin 5 ana zargin sun tsere ne da nufin zama a Turai saboda dalilai na tattalin arziki.

Maitsaron gida ta wasan kwallon kafa ta zaman-ko-ta-kwana ta kungiyar mata ta kasar Drusille Ngako ita ce ta fara bacewa kamar yadda jami’an tawagar Olympic din na Kamaru suka sanar.

Shugaban tawagar Kamarun a wasan na Olympics David Ojong yace abin da ya fara da farko a matsayin jita-jita a karshe ya zama gaskiya kamar yadda ya rubuta a wata wasika da ya aikawa ma’aikatar wasanni ta Kamaru.

Bayan da maitsaron gidan ta fara tserewa sai dan wasan linkaya Paul Ekane Edingue ya bi baya da kuma wasu ‘yan damben boksin 5 suma suka bace.

Dama a watan Yuni wani dan kasar Ethiopia da ya rike fitilar wasan na Olympics Natnael Yemane dan shekara 15 shi ma ya bace.

Karin bayani