Roberto Huth na fama da sankarau

Image caption Roberto Huth

Dan wasan baya na kulob din Stoke City, Roberto Huth, na fama da ciwon sankarau lamarin da ya sa shi zuwa asibiti domin gudanar da gwaje-gwaje a kansa.

Huth, dan shekaru 27, ya je asibiti ne bayan da gwajin farko da aka yi masa lokacin da yake atisaye a filin wasan kulob din a farko makon nan, ya nuna yana dauke da kwayoyin ciwon sankarau.

Manajan Stoke City, Tony Pulis, ya ce: '' A fili take cewa baya jin dadin jikinsa.Muna fata ciwon ba mai tsanani ba ne, kuma zai samu sauki da wuri''.

An hana Huth buga wasan share fagen kakar wasanni ta bana wadda kulob din ya yi da kulob-kulob biyu watau, Torquay da Yeovil Town.

Pulis ya kara da cewa: ''Rashin lafiyarsa wani abin takaici ne ganin cewa muna dab da shiga kakar wasa ta bana.Huth na daga cikin 'yan wasan da ke da muhimmanci a garemu''.

Huth na daga cikin 'yan wasan da suka sa kulob din Chelsea ya lashe gasar Premier sau biyu, sai dai ya koma kulob din Middlesbrough a shekarar 2006.

A shekaru ukun da suka gabata ne ya shiga Stoke City a kan fam miliyan biyar.

Karin bayani