Barcelona na shirin sayen Alex Song

alex song
Image caption Alex Song

Kungiyar Barcelona na shirin neman sayen dan wasan Arsenal dan Kamaru Alex Song.

Rahotanni na nuni da cewa Barcelonan ta nuna sha'awarta ta sayen matashin dan wasan mai shekara ashirin da hudu duk da cewa har yanzu kungiyar ba ta fito fili ta gabatar da bukatarta ta dan wasan ba ya zuwa yanzu.

Song wanda da farko ya je Arsenal a matsayin aro a 2005 yaji dadin yadda Barcelona ta yi sha'awarsa kuma ya zaku yaji abin da zata fada game da sayen nasa.

Saura shekaru uku a kwantiraginsa da Arsenal amma da alamu Barcelona ba za ta biya fam miliyan 15 da Arsenal za ta bukata a kansa ba.

A shekaru biyun da suka gabata Song ya zama daya daga cikin 'yan wasan da Arsenal take ji da su sai dai ana ganin sha'awar da yake yi ta yawan barin baya ya kai hari a lokacin wasa da hakan kan haifar da baraka a bayan ita ce matsalarsa.

Karin bayani