An samu matsala game da sayen Van Persie

Hakkin mallakar hoto
Image caption Van Persie

Kocin Manchester United, Sir Alex Ferguson, ya ce yunkurin da suka yi na sayen dan wasan Arsenal, Robin van Persie, ya ci tura.

Saura watanni goma sha daya dan wasa, mai shekaru 29, ya kammala kwantiraginsa da Arsenal kuma ya ki amincewa da bukatar da kulob din ya yi masa na sabunta kwantiraginsa.

Ferguson ya ce: " Mun taya dan wasan, sai dai da alama Arsenal na tattaunawa da wadansu kulob din a kansa. Ina ganin ba za mu sasanta da Arsenal game da sayen dan wasan ba.''

A ranar 20 ga watan Yuli ne Ferguson ya ce kulob dinsa na shirin sayen Robin van Persie daga Arsenal.

Arsenal ba ta son shiga yarjejeniya da duk kulob din da ba zai taya dan wasa a kan fam miliyan ashirin ba.

Sai dai babu wani bayani game da ko hakan ne ya sanya aka samu matsala tsakanin Arsenal da Manchester United game da cinikin dan wasan.

Karin bayani