Rudisha ya kafa tarihi a tseren mita 800

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption David Rudisha

Duniya baki daya sun juya hankalinsu a ranar Alhamis kan Usain Bolt, sai dai kuma sun ga wani dan wasa wanda ya tabbatar da matsayinsa a cikin tarihin Olympics.

Kodayake Bolt ne ya fi yin fice game da samun lambar zinare a gudun mita 200, sai dai wanda ba a cika jin sa ba David Rudisha, shi ne ya zamo mutum na farko da ya kafa tarihi a gasar Olympics ta bana a London a gudun mita 800.

David Rudisha, dan asalin kasar Kenya, wanda yanzu yake da shekaru 23 ya shiga filin wasanin Olympics ne awannan makon ba tare da mutane da dama sun kula da kwazonsa ba.

Amma ya tabattarwa jama’a dalilin da yasa watakila Lord Coe, shugaban hukumar shirya wasannin Olympics na London ya kirashi mafi hazaka a cikin ‘yan wasan gudu da tsale-tsale na Olympics yayinda ya kafa tarihi na duk duniya da zama mutun na farko da yayi tseren mita 800 cikin minti 1 da dakika 40 (1:40:91)

Wani mai yiwa BBC sharhi kan wasanni wanda shi ma ya taba karbar lambar yabo ta wasanin Olympics Steve Cram bai yi mamakin bajintar da Rudisha ya nuna ba a tseren ba.

Cram ya ce: “wannan abun mamaki ne! wannan shi ne tseren gudun mita 800 da ba a taba ganin wani yayi irinsa ba.”

Shugaban wasanin London Coe ne ya kafa trihin farko na tseren a shekara ta 1981 a cikin minti 1 da dakika 41 (1:41:91) bayan shekaru 16 ne aka samu wani dan asalin kasar Kenya mai suna Dane Wilson Kipketer wanda ya doke shi da lashe tseren cikin 1:41:11

Bayan shekaru goma, sai Rudisha ya taka rawar gani amma zamu jira muga abun da zai tabuka a Brazil a gasar Olympics mai zuwa.