'Yan damben boksin din Kamaru na son zama a Birtaniya

Dan wasan damben boxing dan Kamaru
Image caption Dan wasan damben boxing dan Kamaru

'Yan damben boksin 'yan jamhuriyyar Kamaru da suka tsere daga masaukin 'yan wasan Olympics a London, sun shaidawa BBC cewa suna son cigaba da zama a London don bunkasa sana'arsu.

'Yan damben su biyar sun gana da BBC ne a wani gurin da ba a bayyana ba, bayan sun shafe fiye da mako guda da bacewa.

Hukumomi a kasar Kamaru na zargin 'yan damben da son zama 'yan cirani a Birtaniya.

'Yan damben dai sun ce sun tsere daga masaukinsu ne bayan wasu manyan jami'an tawagar sun yi musu barazana.

A makon jiya ne mai wasan ninkaya Paul Ekane Edingue da mai tsaron gida Drusille Ngako suka yi batan dabo daga masaukin 'yan wasan.

Alawus-alawus

'Yan wasan Thomas Essomba da Christian Donfack Adjoufack da Abdon Mewoli da Blaise Yepmou Mendouo da kuma Serge Ambomo sun ce 'yan wasa a Kamaru ba sa samun goyon bayan da ya kamata.

A hirar da suka yi da BBC, Essomba ya ce suna neman wadanda za su dauki nauyinsu don bunkasa sana'oinsu tare da nema musu takardun zama a Birtaniya.

"Muna son zama a nan ne ba don ba ma son kasarmu ba, a'a sai don muna son mu yi wasannin dake faranta mana rai."

"Muna so mu kware a wasanninmu, saboda haka ba za mu iya komawa kamaru ba.

Idan mun koma ba za mu cigaba da yin wasannin ba."

Mendouo ya ce jami'an tawagarsu basu kyautata musu ba a lokacin gasar Olympics.

Haka kuma an sami banbanci game da kudaden alawus-alawus da aka yi musu alkawari, wanda aka raba shi gida biyu.

Jami'an da suka rakomu sun yi mana barazana. Inji Mendouo.

Ya cigaba da cewa " Lokacin da wani dan wasa bai samu nasara ba, sai aka bukaci ya mika fasfonsa."

Sai dai shugaban tawagar Kamaru, David Ojong ya musanta zargin.

Inda ya ce ba a taba yi musu wata barazana ba, suna dai kawai neman uzuri ne na tserewar da suka yi.

'Yan wasan dai na da takardun zama a Birtaniya wato visa na wata shida, wanda zai kare a watan Nuwanba.