BBC navigation

Kungiyar Wolves ta ki sayarwa Sunderland Fletcher

An sabunta: 14 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 21:34 GMT
steven fletcher

Steven Fletcher

A karo na uku kungiyar Wolves ta ki amincewa da bukatar Sunderland ta sayar mata da dan wasanta Steven Fletcher.

A karon farko sunderland ta taya dan wasan mai shekara 25 fam miliyan 10, a karo na biyu ta saye shi fam miliyan 12 Wolves din bata sayar ba.

Yanzu kuma Sunderland din ta kara taya dana wasan a wani farashin amma kasancewar kudin ba su kai fam miliyan 15 da Wolves din ta sa a kansa ba bata sallamaba.

Fletcher ya nuna aniyarsa ta tafiya Sunderland tun a lokacin da kungiyar ta taya shi fam miliyan 12.

Dan wasan wanda ya ciwa Wolves da ta fado daga matakin Premier kwallaye 12 a wasannin 26 yana da sauran shekaru 2 a kwantiraginsa.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.