BBC navigation

Arouna Kone ya koma Wigan

An sabunta: 15 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 13:25 GMT

arouna kone

Kulob din Wigan ta gama yarjejeniyar siyan dan wasan gaba dan asalin kasar Ivory Coast Arouna Kone daga kulob din Levante a kudin da basu fayace ba.

Dan wasa mai shekaru 28 ya ci kwallaye 15 a wasanni 34 a kakar wasannin bara, hakan ya taimaka wa Levante ta kai mataki na shida a wasannin La Liga lokacin da Sevilla ta bayar da shi aro.

A karshen kakar bana ne aka tabbattar da komawar shi ta dindindin daga Sevilla zuwa Levante.

Ya koma kulob din ne washe garin da manajan Wigan Roberto Martinez ya yi aron dan wasan tsakiya Ryo Miyaichi daga Arsenal.

Kone wanda ya buga wa kasarsa har sau 35 ya sa hanu a kwantiragi na tsawon shekaru 3 da Wigan kuma ya jefa kwallaye 9 a raga a duk tsawon lokacin day a shafe a kulob din.

Har yanzu Martinez na neman wanda zai maye gurbin dan wasan gaba wanda ya koma Fulham bayan kwantiraginsa ya kare.

Wigan ta kuma sayi mai tsaron gida Ivan Ramis daga Mallorca da dan wasan tsakiya Fraser Fyvie daga Aberdeen.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.