BBC navigation

Mourinho ya ce ya kamata a sauya masa lakabi

An sabunta: 15 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 16:28 GMT
jose mourinho

Jose Mourinho

Kocin Real Madrid Jose Mourinho ya nemi da a sauya lakabin da ake kiransa da shi the 'Special One' wato 'na musamman' a madadinsa a daukaka shi zuwa 'kai kadai ne' wato the 'Only One'.

Mourinho yana ganin ya cancanci sabon lakabin ne saboda shi kadai ne kocin da a tarihi ya sami nasarar daukan kofunan manyan gasar lig-lig na Turai uku.

A kakar wasannin da ta wuce kocin ya dauki Kofin La Liga na Spain da Real Madrid kari a kan Kofin Lig din Seire A biyu da ya dauka da Inter Milan da kuma Kofin Premier na Ingila da ya dauka da Chelsea.

Bayan wannan ma kuma ga Kofin lig din kasarsa Portugal da ya dauka da kungiyar Porto har sau biyu sannan kuma ga Kofin Zakarun Turai da ya dauka sau biyu.

Mourinho ya ce a shekarar 2010 an zabe shi a matsayin kocin na daya a duniya ,a 2011 an zabe shi na biyu a duniya a don haka yanzu baya damuwa da matsayin da yake.

Yace yanzu yana gab da cika shekara 50 a duniya kuma ji yake kamar yanzu ya fara sana'ar horadda 'yan wasa.

'yan jaridar Birtaniya ne suka sanya masa lakabin 'na musamman' din bayan da ya kira kansa haka ya yin wani taron manema labarai bayan da ya dawo Chelsea daga Porto a 2004 inda ya sani nasarar daukar kofin Zakarun Turai.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.