BBC navigation

Fabrice Muamba ya daina wasan kwallon kafa

An sabunta: 15 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 15:32 GMT
fatrice muamba

Fatrice Muamba

Dan wasan tsakiya na Bolton Fabrice Muamba ya sanar da ritayarsa daga wasan kwallon kafa.

Muamba dan shekara 24 ya yanke jiki ne ya fadi sakamakon ciwon bugun zuciya da ya same shi farat daya lokacin da ake tsakar wasan gab da na kusa da na karshe na cin Kofin kalubale na hukumar kwallon kafa ta Ingila tsakanin Bolton da Tottenham ranar 17 ga watan Maris.

Muamba yace a makon da ya wuce ne ya je Belgium domin neman karin shawara daga wani kwararren likitan zuciya a game da ciwon nasa, amma likitan bayanin da ya samu daga likitan ba abu ne da ya yi fatan ji ba wanda dalilinsa ya dauki matakin sanar da yin bankwa nan da sana'ar wasan kwallon kafa.

Sanarwar ritayar tasa ta zo ne watanni shida bayan da ya gamu da ciwon bugun zuciyar wanda a lokacin likitoci suka ayyana cewa ya mutu tsawon mintina 78.

Daga nan ne aka kwantar da shi a sashen kulawa da marassa lafiyar da ke cikin halin rai kwakwai mutu kwakwai tsawon makwanni hudu kafin a sallameshi bayan da ya farafado ranar 16 ga watan Afrilu.

A ranar 2 ga watan Mayu ne kuma Muamba ya bayyana a filin wasasu na Reebok kafin karawar Bolton da Tottenham ya bayyana godiyarsa ga magoya bayan kungiyar ta Bolton.

Fabrice Muamba ya fara wasan kwallon kafa ne a Arsenal daga nan kuma ya koma Bermingham kafin daga Bisani ya koma Bolton inda ya yi shekaru hudu.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.