BBC navigation

Real Madrid na gab da kammala sayen Modric

An sabunta: 16 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 21:29 GMT
luka modric

Luka Modric

Real Madrid na gab da kammala cimma bukatarta ta sayen Luka Modric daga kungiyar Tottenham bayan da ta kara farashin da ta taya shi zuwa fam miliyan 30.

Ana sa ran dan wasan mai shekaru 26 ya tattauna da shugabannin kungiyar ta Real Madrid a kwanakin dake tafe bayan da Real madrid din ta farfado da maganar sayen dan wasan bayan da adamaganar ta ci tura.

Nan da 'yan sa'oi ne ake saran Modric zai je a duba lafiyarsa a Madrid din da kuma tattaunawa a kan sharuddan kwantiragin nasa.

Kocin Tottenham Andre Villas-Boas na fatan za su kammala batun sayar da dan wasan nan bada daewa ba.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.