BBC navigation

Eneramo ya koka da rashin daukarsa Super Eagles

An sabunta: 17 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 17:41 GMT
Michael Eneramo

Michael Eneramo

Dan wasan gaba Michael Eneramo ya ce ya yi amanna ya cancanci a sake kiranshi ya shiga tawagar Najeriya bayan da ya ci wa kungiyarsa ta Sivasspor kwallaye goma sha biyar a kakar wasanni ta bara.

Hakan dai ya sa dan wasan mai shekaru ashirin da shida da haihuwa ya zama dan Najeriyar da ya fi tashe a Turkiyya.

Sai dai kuma yayin da yake zabar 'yan wasan da za su bugawa Super Eagles a wasannin neman gurbin zuwa Gasar cin Kofin Duniya ta 2014 da kuma Gasar cin Kofin Kasashen Afirka ta 2013, kocin tawagar, Stephen Keshi, ya tsallake sunan Eneramo.

"Na ji takaici da aka yi watsi da ni. Ban san me zan kara yi ba dona dauke ni", inji dan wasan.

Ya kuma kara da cewa "Na san akwai 'yan wasa masu kyau amma ya kamata a baiwa kowa dama ba tare da yin la'akari da gasar da yake buga wasa ba".

Sau goma sha daya Eneramo ya bugawa Najeriya wasa, ya kuma ci mata kwallaye hudu--ta baya-bayan nan wadda ya ci yayin wasan Super Eagles da Madagascar shekaru biyu da suka wuce a Calabar.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.