BBC navigation

Song ya kulla kwantiragin shekaru biyar da Barca

An sabunta: 20 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 17:00 GMT

Dan wasa Alex Song yana kokawar karbe kwallo.

Dan wasan Arsenal da Kamaru Alex Song ya koma Barcelona bayan da ya kammala tattaunawa da gwajin lafiya a kasar Spain.

Dan wasan mai shekaru 24 ya sanya hannu kan kwantiragin shekaru biyar a Nou Camp bayan da Barcelona ta amince ta biya Arsenal fan miliyan 15.

Song wanda kwantiraginsa ke dauke da wata yarjejeniyar ta kusan fan miliyan 63, ya kammala gwajin lafiya ne a ranar Litinin.

A yanzu Arsenal ta mayar da hankali ne wurin karbar aron dan wasan Madrid Nuri Sahin na shekara guda domin maye gurbin Song - rahotanni sun ce akwai yiwuwar su cimma matsaya da Real Madrid.

Song bai taka leda a wasan da Arsenal ta tashi 0-0 da Sunderland ba a ranar Asabar, bayan da kungiyar ta tabbatar da cewa ta kulla yarjejeniya da Barcelona domin sayar da shi.

A ranar Talata ne ake saran Barcelona za ta gabatar da shi a gaban 'yan jarida.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.