BBC navigation

Carvalho zai koma QPR daga Real Madrid

An sabunta: 22 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 12:25 GMT
carvalho

Ricardo Carvalho zai hade da Bosingwa a QPR

Kungiyar Queens Park Rangers ta Ingila da Real Madrid ta Spain sun amince akan yarjejeniyar bada aron tsohon dan wasan Chelsea Ricardo Carvalho na tsawon kakar wasa guda.

Dan wasan Real Madrid din mai shekaru talatin da hudu ya amince ya sake dawowa Ingila don taka leda da QPR.

A ranar Talata kuma QPR da Spurs suka kulla yarjejeniyar cefanarda Micheal Dawson akan pan miliyon bakwai da rabi.

Mark Hughes kocin QPR na kokarin kara karfin 'yan wasansa na baya, bayan da suka sha kashi daci biyar da nema a hannun Swansea a ranar Asabar.

Canza shekara Dawson dai ana saran za a kamalla shi cikin 'yan sa'o'i masu zuwa bayan an gwada lafiyar dan kwallon.

Carvalho ya taka leda a Chelsea lokacin da Jose Mourinho yake kocin kulob din inda suka lashe gasar Premiya a shekara ya 2005 da kuma 2006.

Kenan Carvalho zai hade da tsohon abokin wasansa a Chelsea Jose Bosingwa wanda shima ya koma QPR.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.