BBC navigation

Paralympics: Jordan ta kori 'yan wasa 3

An sabunta: 23 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 17:08 GMT

Bajen gasar wasannin Olympics ta birnin london

Kwamitinin wasannin Olympics na kasar Jorda ya kori wasu 'yan wasa uku dake cikin tawagar da zata wakilci kasar a gasar Olympics ta masu nakasa wadda za a soma a London a makon gobe bisa zargin aikata lalata.

Ana zargin Mai horarda 'yan wasa Faisal Hammash da 'yan wasar daukar karfe Umar Sami da Mutaz Al-Junaidi da jerin laifukan da suka shafi lalata cikin har da yunkurin yin fyade da kuma leken mata suna tube kaya a garin Antrin na Ireland ta arewa inda suke atisaye.

Wasu 'yan mata biyu da mata biyu ne suka kai koke kan su.

An dai kama mutanen ne ranar litinin sa'annan aka gurfanar da su a gaban kotu jiya laraba kodayake an bayarda Belin su ga Ofishin Jekadancin Jordan dake London bisa sharadin zasu mayarda su domin cigaba da shara'ar a watan Oktoba.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.