BBC navigation

An soke nasarorin Armstrong na Tour de France

An sabunta: 24 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 16:39 GMT
LLance Armstrong, dan wasan tseren keke na Tour de France

Lance Armstrong, dan wasan tseren keke na Tour de France

Hukumar yaki da shan kwayoyi masu kara kuzari ta Amurka ta soke nasarorin da Lance Armstrong ya samu a tseren keke na Tour de France.

Haka kuma hukumar ta haramta masa wasan tseren na Tour de France a tsawon rayuwarsa.

Hakan ya biyo bayan kin amincewar da Armstrong ya yi na kalubalantar zargin da ake masa na amfani da kwayoyin kara kuzari.

Shugaban hukumar John Fahey ya ce kin kalubalantar zargin da Armstrong ya yi na nuna cewa akwai kamshin gaskiya a zarge-zargen da ake masa.

" A fahimta ta tunda shedar da ake da ita, ta shafi sana'arsa wacce ya samu nasarori sau bakwai a cikinta, to dole ne a soke dukanninsu. " A cewar Fahey.

Tun da fari a wata sanarwa da Armstrong ya fitar ya ce, ba zai kalubalanci zarge-zargen amfani da kwayoyin kara kuzarin da hukumar ta Amurka ke yi masa ba.

Ya jaddada cewa bai aikata laifukan amfani da kwayoyin ba, amma ya damu da zarge-zargen da ba su da tushe balle makama.

Ba Amurken dan shekaru 40 ya kuma ce, ba zai biyewa abin da babu adalci a cikinsa ba.

Lance Armstrong ya sami nasarorin tseren keke na Tour de France ne daga shekarun 1999 zuwa 2005.

Hukumar ta ce za ta bayyana shedar da take da ita game da Armstrong a lokacin da ya kamata.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.