BBC navigation

Tottenham za ta sayi Yann M'Vila daga Rennes

An sabunta: 27 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 16:56 GMT
Yann M'Vila

Yann M'Vila

Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham ta yi tayin sayen Yann M'Vila daga Rennes a kan kudi sama da fam milyan 12.

Sai dai kulob din na Rennes na neman milyan 15 ne.

Kungiyar ta Faransa ta nemi da a tautauna kai tsaye a kan batun sayen dan wasan.

Wata kungiyar da ba a bayyana sunan ta ba, kuma ba ta Arsenal ba ce, na neman sayen M'Vila.


Tottenham ta kasance ita kadai ce a yanzu ke zawarcin M'Vila, bayan ya ki amincewa ya koma kulob din Zenit St. Petersburg da kuma Shakhtar Donestsk.

M'Vila ya yi wa kungiyar Rennes da Faransa wasanni sittin da daya a kakar wasannin bara, sai dai ana sa ran zai yi wasanni uku cikin hudu na nahiyar turai a shekarar 2012.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.