BBC navigation

Real Madrid ta sayi Luka Modric daga Spurs

An sabunta: 27 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 09:15 GMT
Luka Modric

Luka Modric

Kulob din kwallon kafa na Real Madrid ya cimma yarjejeniya da kulob din Tottenham kan sayen dan wasan tsakiyan Tottenham, Luka Modric a kan kudi kimanin fam miliyan 30.

Dan wasan kasa da kasa dan Croatia mai shekaru 26 zai je kasar Spaniya ranar Litinin don a duba lafiyarsa.

Haka kuma kulob din Tottenham ya fitar da sanarwa cewa za su shiga taimakekeniya da Real Madrid.

Inda a karkashin yarjejeniyar kulob-kulob din biyu za su dinga aiki tare a kan abubuwan da suka shafi 'yan wasa da horarwa da kuma wasu harkokin kasuwanci.

Game da sayar da dan wasan, shugaban Tottenham Daniel Levy yace " Luka gwarzon dan wasa ne a gare mu, kodayake ba ma son rabuwa da shi, amma muna farin cikin cewa Real Madrid zai koma"

Luka Modric ya koma Tottenham daga kulob din Croatia a shekarar 2008 a kan kudi fiye da fam miliyan 16.

Shugaban Real Madrid, Florentino Perez Rodriguez ya bayyana cewa " Muna farin ciki da maraba da Luka tare da aiki kafada-da- kafada da Tottenham a cikin shekaru masu zuwa."

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.