BBC navigation

Villa ta kasa sayen Christian Benteke

An sabunta: 28 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 15:18 GMT
Jami'in Aston Villa Alex Mcleish

Alex Mcleish

Kungiyar kwallon kafa ta Aston Villa ba ta yi nasarar sayen Christian Beneteke daga kungiyar Genk ba.

Aston Villa ta yi tayin sayen dan wasan dan kasar Belgium, mai shekaru 21 wanda kuma ya ci kwallo uku a wasanni biyar na wannan kakar wasannin a kan fam miliyan biyar da rabi.

Eris Kismet shi ne dillalin dake kula da cinikin dan wasan: "Gaskiya shugabanin kungiyar ta Villa na kwatanta shi da Eden Hazard, amma shi wasa daya ya bugawa Belgium."

Aston Villa ta ki cewa komai game da batun.

Benteke shi ne wanda ya ci kwallo hudu a lokacin wasa tsakanin Belgium da Netherlands da aka tashi hudu da biyu.

Kismet ya kuma yi watsi da hasashen da ake yi na cewa dan wasan da ya zuwa kwallo 16 a kakar wasannin da ya gabata, ya je yajin aiki a lokacin da ji cewa Genk ya ki amincewa da tayin na Villa.

Paul Lambert jami'i ne na Ashton Villa kuma ya amince yana neman sabbin 'yan wasan gaba, amma ya ce babu batun zuwa kulob din Tottenham don zawarcin Jermain Defoe ko zuwa Sunderland don tayin sayen Kenwyne Jones.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.