BBC navigation

Man City na kusa da daukar sabon mai tsaron gida

An sabunta: 29 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 18:23 GMT

kungiyar Man. City ta na bikin lashe kofi

Kungiyar Manchester City na gab da sayen dan wasan baya na kasar Serbia Matija Nastatic daga Fioretina akan kudi kimanin Fam miliyan 12.

Manajan Kungiyar ta City Roberto Mancini dai ya dade yana son ya ga sayo dan wasan mai shekaru 19.

Shi kuwa tsaron gidan City din Stefan Savic ana sa ran ya bar kulob din a yayinda Mancini ke kokarin karfafa kungiyar wadda ke rike da kambun gasar Premier Yanzu haka.

Shima dan wasan gaba Roque Santa Cruz dan shekaru 31 zai iya barin sa kafin karewar wa'adin sayen sabbin 'yan wasa a ranar Jumu'a, inda kungiyoyin Malaga da Real Betis kowacce ke zumudin ganin ta karbi dan wasan aro.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.