BBC navigation

Yau za a fara gasar wasannin paralympics

An sabunta: 29 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 09:21 GMT
Alamun gasar wasannin nakasassu ta Paralympic

Alamun gasar wasannin nakasassu ta Paralympic

Dubban mutane ne suka yi dandazo domin tarbar wutar gasar nakasassu ta Paralympic a birnin London.

Tun a daren ranar Talata ne mutane suka yi dafifi a kan hanyar da za a bi da wutar daga Stoke Mandeville zuwa filin wasa, inda za a yi bikin bude gasar.

An samu jinkiri na kusan sa'oi biyu kafin wutar ta isa arewacin London, sai dai masu shirya gasar sun ce suna kokarin famshe lokacin.

Ana sa ran Sarauniyar Ingila da Duke da Duchess na Cambridge za su halarci bikin bude gasar da za a fara da karfe 8:30 na daren yau.

Jama'ar dai sun taru a kasuwar dake Aylesbury da Buckinghamshire don kallon fara tafiya da wutar, yayin da wasu dubban ke jira a kan hanyar da za a bi da wutar.

Mutane 580 ne aka shirya za su karbi wutar a zagayen da za a yi da ita zuwa filin wasa inda za a yi bikin bude gasar nakasassun ta Paralympic.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.