BBC navigation

Za a fitar da rukunan gasar champions league

An sabunta: 30 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 08:23 GMT
Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ce ke rike da kofin zakarun Turai

Akwai yiwuwar za a hada kulob din Manchester United da kulob-kulob din da suka ci gasar champions league na Jamus da Spaniya da kuma Italiya, idan an tashi fitar da rukunan champions league a yau Alhamis.

Kulob din da ya lashe gasar Premier league wato Manchester City zai kasance a tukunya ta biyu kuma akwai yiwuwar karawarsu da Borussia Dortmund da Real Madrid da kuma Juventus.

Kulob-kulob din dake rike da kofunan gasar Champions wato Chelsea da Arsenal and Manchester United za su kasance a tukunya ta farko.

Kulob-kulob guda 32 ne za a zuba a tukwane hudu, sannan a raba su zuwa rukunai hudu dake kunshe da kulob-kulob takwas-takwas.

Kulob din da ya lashe gasar champions na Scottland wato Celtic, shi ma yana cikin rukunan da za a raba, saboda nasarar da ya samu a kan kulob din Helsingborgs.

Manchester City zai kasance a tukunya na biyu saboda nasarar da kulob din ya samu a gasar Uefa bai kai na tkwarorinsa dake tukunya ta daya ba.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.