BBC navigation

Real Madrid ta lashe gasar Super Cup

An sabunta: 30 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 12:51 GMT
Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta doke Barcelona da ci biyu da daya, abinda ya kaita ga daukar kofin gasar Super Cup na Spaniya.

Real ta yi amfani da kuskure biyun da aka samu, abin da ya sa nan da nan ta samu ci biyu da nema bayan an dawo hutun rabin lokaci a karawar da suka yi a filin wasa na Bernabeu.

'Yan wasan Real Madrid, Gonzalo Higuain da Cristiano Ronaldo ne suka samu zura kwallo a ragar Barcelona a taka ledar.

Sakamakon wasanni biyun da suka buga ya nuna cewa an tashi wasan kowacce kungiya na da ci 4-4 kasancewar Barcelona ta doke Real da ci 3-2 a wasan farko. Sai dai Real din ta samu nasarar lashe kofin kasancewar ta zira kwallaye mafiya yawa a gidan Barcelona.

Kashin da Barcelonar da sha na nufin sabon kocinsu Tito Vilanova bai samu damar daukar wa kulob dinsa kofi ba.

Wannan ne karo na farko da Real Madrid ta lashe gasar ta Super Cup tun shekarar 2008.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.