BBC navigation

Manchester City ta sayo Maicon daga Inter Milan

An sabunta: 31 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 17:22 GMT
maicon

Maicon ya yar da jesin Inter Milan

Kungiyar wasan kwallon kafa ta Manchester City ta sayo dan wasan kwallon kafa Maicon daga Inter Milan.

Kungiyar ta dauki shahararren dan wasan dan kasar Brazil ne akan kudin da ba a bayyana ba.

Mai horar da 'yan wasan kungiyar ta Manchester city ya taba aiki da dan wasan mai kimanin shekaru 31 a kakar wasanni biyu, wato a tsakanin shekarar 2006 da 2008 a lokacin da yake tare da kungiyar Inter Milan.

Dan kasar Brazil din ya fara wasa ne a kungiyar Cruziero da ganan ya koma Monaco, kafin daga bisani ya sauya sheka zuwa Inter Milan, inda ya buga musu wasanni 235.

Maicon wanda dan wasan baya ne, ya kan kuma kai hare-hare, inda ya jefawa kungiyar Inter Milan kwallo 20 a raga.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.