BBC navigation

An janye jan katin da aka baiwa Huddlestone

An sabunta: 4 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 18:31 GMT

Dan wasan tsakiya na Tottenham Tom Huddlestone

An janye katin korar da aka baiwa dan wasan tsakiya na Tottenham Hotspur Tom Huddlestone a lokacinda kungiyar ta buga wasa da Norwich City ranar Assabar.

Wannan dai ya biyo ne bayan nasarar da Kungiyar Tottenham ta samu a daukaka kararda tayi ga baiwa dan wasan jan kati zuwa ga Hukumar Wasan kwallon Kafa ta Ingila( FA).

Alkalin wasan Mark Halsey ne ya sallami Huddleson daga fage saboda taba dan wasan Norwich Jonny Howson da yayi a minti na 90 na wasan ta gasar Premier League da tottenham din ta karbi bakunci ranar Assabar; wadda ta tashi kunnen doki 1-1.

Hukumar ta FA a yanzu ta soke haramcin buga wasanni uku da aka sakawa dan wasan; don haka zai buga wasan da za su buga da Reading ranar 16 ga watannan.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.