BBC navigation

U-20: Amurka ta doke Najeriya

An sabunta: 4 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 16:04 GMT

Shugaban hukumar FIFA Joseph Blatter

Amurka ta doke Najeriya da ci 2-0 ranar talata a wasan gab da na karshe ta gasar kwallon kafa ta cin kofin duniya ta mata 'yan kasa ga shekaru 20 dake gudana a kasar Japan.

'yar wasan Amurkar Morgan Brian ce ta fara jefa kwallo a ragar Najeriya a rabin lokaci na farko, yayinda takwararta Kealia Ohai ta kara ci na biyu bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, abinda ya baiwa Amurka damar kai matakin karshe na gasar a karo na uku.

Da hakan yanzu Amurkar zata kara da ko dai mai masaukin baki wato Japan ko kuma mai rike da kambun gasar watau Jamus, a wasan karshe ta gasar ranar Assabar mai zuwa.

Najeriya wadda ta buga wasan karshe ta gasar da kasar Jamus shekaru biyunda suka wuce, za ta buga wasan neman na ukku da duk kasarda aka doke wasan gab da na karshe ta biyu tsakanin Japan da Jamus din.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.