BBC navigation

CAN 2013:'Akwai bukatar hadin kan 'yan wasan Kamaru'

An sabunta: 10 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 15:30 GMT

Kungiyar Kwallon kafa ta kasar Kamaru Indomitable Lions

Daraktan sashen horarda 'yan wasa na Hukumar kwallon kasar Kamaru yace akwai bukatar 'yan wasa da jami'ai su sansanta domin cigaban kungiyar kwallon kafar kasar ta Indomitable Lions.

Robert Atah yayi wadannan kalaman ne bayan Kamaru ta sha kashi da ci 2-0 a hannun Cape Verde a wasan farko na zagayen karshen na gasar neman cancantar shiga gasar cin kofin kasashen Nahiyar Afrika ta 2013.

Yace matsalar ta samo asalin daga baiwa Samuel Eto'o mukamin Kyaftin da aka yi alhali har yanzu tsohon kyaftin Rigobert Song yana buga wasa,inda ya kara da cewar akwai rarrabuwar kawuna sosai a cikin kungiyar tsakanin 'yan wasa da kuma tsakani Jami'ai.

Eto'o dai yaki amsa kiranda aka yi masa na shiga wasanda Kamaru ta buga da Cape Verde saboda wani yajin aikin buga wasa na watanni takwas da ya shiga a bara; kuma yanzu Kamaru na bukata ta lashe wasan na biyu da za su buga da Cape Verde din a watan gobe da ci ukku kafin ta samu cancantar shiga gasar.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.