BBC navigation

Ingila ta kira wasu 'yan wasa uku horo

An sabunta: 10 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 14:15 GMT
Mai horar da 'yan wasan Ingila, Roy Hudgson

Mai horar da 'yan wasan Ingila, Roy Hudgson

Ingila ta kira Rahem sterling na Liverpool da Jake Livermore na kulob din Tottenham da kuma Adam Lallana na Southampton cikin tawagar 'yan wasanta.

Mai horar da 'yan wasan Ingila Roy Hudgson ya kira 'yan wasan ne bayan 'yan wasa biyu, Theo Walcott da Daniel Sturridge sun kamu da rashin lafiya.

Hudgson yace Walcott da bashi da lafiya sosai ya koma kulob dinsa, amma yana cike da fatan cewa, Sturridge zai samu saukin ciwon cikin dake damunsa kuma a fafata da shi.

Sai dai ya ce ba lallai ba ne 'yan wasan uku da aka kira daga baya su fafata a karawar da kasar za ta yi da Ukraine a ranar Talata.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.