BBC navigation

Olympics: Burtaniya ta yi faretin samun nasara

An sabunta: 10 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 16:53 GMT

Faretin 'yan wasan Olympics na Burtaniya

Dubun dubatar mutane ne suka yi cincinrindo a titunan birnin London ranar Litinin domin kallon wani fareti da 'yan wasanda suka wakilci Birtaniya a gasannin Olympics da Paralympics na shekara ta 2012 suka yi a birnin.

Kimanin 'yan wasa 800 da suka shiga wasan daga kasar ta Burtaniya ne suka zagaya titunan birnin na London a cikin budaddun motoci domin murnar nasarorin da suka samu a gasannin biyu; da kuma nuna kawo karshen bikin wasannin na makonni shida.

Y'an wasan sun kammala faretinne a fadar sarauniyar Ingila ta Buckinham inda aka yi kade-kade da wake-wake da kuma jawabai; yayinda jiragen kanfanin zirga-zirgar jiragen saman Burtaniya suka yi wani shawagi a saman fadar domin karrama 'yan wasan tare da sakin hayaki mai launukka uku da tutar Burtaniya ke da.

Duka dai tawagogin Olympics da na Paralympics na kasar ta Burtaniya sun zo na uku ne a jerin kasashenda suka samu lambobin yabo a wasannin na London Olympics.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.