BBC navigation

Walcott da Sturridge ba su samu halartar horo ba

An sabunta: 10 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 11:19 GMT
Theo Walcott

Theo Walcott

'Yan wasa Theo Walcott da Daniel Sturridge ba su samu halartar horo na 'yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Ingila ba, wanda ake yi yau litinin saboda rashin lafiya.

A gobe Talata ne dai kulob din zai kara da kasar Ukraine a wasan share fagen shiga gasar cin kofin duniya.

Dan wasan gefe na kulob din Arsenal Walcott da dan wasan gaba na kulob din Chealsea Sturridge sun bayyana cewa ba su da lafiya cikin dare.

Kuma rashin halartar 'yan wasan masu shekaru 23, na nufin 'yan wasa 18 ne kadai suka halarci sansanin horon na karshe.

Dama can 'yan wasan baya John Terry da Ashley Cole ba za su samu halartar taka ledar na gobe ba, saboda raunin da suka samu a agararsu.

A ranar Lahadi kungiyar kwallon kafa ta sanar da cewa John Terry ba zai samu shiga gasar ba.

Mai horar da 'yan wasan kungiyar kwallon kafa na Ingila, Roy Hodgson ya kira 'yan wasan baya Phil Jagielka da Gary Cahill saboda rashin halartar Terry.

Inda ake ganin Cahill ne zai maye gurbin Terry.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.