BBC navigation

Kocin 'yan wasan Ingila zai yi murabus.

An sabunta: 11 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 17:16 GMT
charles  van commenee mai horar da yan wasan Ingila

charles van commenee mai horar da yan wasan Ingila


Mai horar da 'yan wasan motsa jiki na Birtaniya, Charles van Commenee zai yi murabus, bayan tawagar da ya tafi da ita gasar Olympics ta kasa cimma yawan lambobin yabon da ya sa ran samu.

Birtaniya ta ce Van Commenee zai bar mukaminsa a watan Disamba, idan kwantiraginsa ya kare.

Kociyan dan kasar Poland mai shekaru 54 ya sa ran samun lambobin yabo takwas, ciki har da lambar zinare guda daya a gasar Olympic na shekarar 2012 da aka kammala a London.

Sai dai tawagar tasa ta samu lambobi shida.

A wata sanarwa da aka fitar, kociyan ya ce aikinsa na bukatar " Sabon jini da sabuwar dabara" don ganin sun samu nasara a gasar cin kofin duniya a shekarar 2017.

Kodayake wasu 'yan wasa sun kare irin rawar da Van Commenee ya taka.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.