BBC navigation

Matasan 'yan wasa na fadi-tashi a gasar premier-Hodgson

An sabunta: 11 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 14:50 GMT
Mai horar da 'yan wasan Ingila, Roy Hodgson

Mai horar da 'yan wasan Ingila, Roy Hodgson

Mai horar da 'yan wasan Ingila, Roy Hodgson ya ce manyan 'yan wasa matasa na ingila na fadi-tashin ganin sun yi fice a fagen gasar premier.

A cewarsa, a wannan kakar wasannin sama da kashi 35 na 'yan wasan Ingila ne cikin 349 suka taka leda a gasar cin kofin Premier League.

Manajan ya ce " Wasan Premier League ya kayatar, sai dai ya kunshi yawancin manyan 'yan wasan turai ne".

Ya kara da cewa "Shahararrun 'yan wasa matasa na fuskantar matsaloli wajen samun shiga cikin kungiyar saboda kasancewar kwararu da su ka shige gabansu."

Shekaru goma da fara gasar Premier League, cikin 'yan wasa 544 da suka taka leda, 391 ko kusan kashi 72 cikin dari turawan Ingila ne.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.