BBC navigation

Keshi ya bukaci 'yan wasan Najeriya su zage dantse

An sabunta: 11 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 09:19 GMT
Mai horar da 'yan wasan Najeriya, Stephen Keshi

Mai horar da 'yan wasan Najeriya, Stephen Keshi

Mai horar da 'yan wasan Najeriya, Stephen Keshi ya bukaci 'yan wasan kwallon kafa na kasar da su zage dantse tare da nuna kwarewa ko kuma su fice daga tawagar.

Mista Keshi ya yi wannan furuci ne bayan 'yan kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles, ba su taka wata rawar a zo a gani ba, a karawar da suka yi da kasar Liberia.

A wasan cancantar shiga gasar cin kofin nahiyar Afrika da aka buga a karshen mako a Afrika ta Kudu, Najeriyar da Liberiar sun tashi ci biyu da biyu.

Keshi ya shaidawa BBC cewa " Wani lokaci sai na ga tamkar babu kyakkyawan shiri da zakuwa a yadda suke wasa, kuma abu ne da ba zan lamunta ba. "

"Dole su sauya yadda suke taka leda domin muna da hanyar da muke bi mai sauki kuma muna son kowa ya bi tare da mutunta ta."

Najeriya dai bata samu shiga gasar cin kofin Nahiyar Afrika ba, wanda kasashen Equatorial Guinea da Gabon suka dau bakunci.

Abin da ya kai ga korar mai horar da 'yan wasan na Super Eagles wato Samson Siasia.

Mai horar da 'yan wasan kuma tsohon mataimakin mai horar da 'yan wasa na kasa da kasa, wanda ya karbi jan ragamar kungiyar, ya nemi 'yan wasan su farka daga barcin da suke yi.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.