BBC navigation

Kurket: Ingila ta doke Afrika ta Kudu

An sabunta: 13 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 08:57 GMT
Tambarin wasa Kurket Twenty20

Tambarin wasa Kurket Twenty20

Ingila ta doke kasar Afrika ta Kudu a gasar Kurket na Twenty na kasa da kasa.

Kuma a yau za ta kara da pakistan da kuma Australia a Sri Lanka a shirye-shiryen fara gasar cin kofin gasar ta duniya.

'Yan wasa Craig Kieswetter da Jos Buttleran ne suka taimaka wa tawagar Ingila wajen lashe gasar.

Nasarar ta sa Ingila ta karbe matsayin Afrika ta Kudu, inda ta zama kasa ta farko a jerin kasashen da suka kware a wasan Kurket, wanda majisar wasan ke fitarwa.

Hakan ya sa Ingila ta nufi Sri Lanka da kwarin guiwa don kare kambunta, a gasar duniya ta Kurket na Twenty20.

Ingila ta yi rawar gani a wasan duk da tsaiko na ruwan sama da aka samu a yayin wasan da aka yi a yankin Birminghan.

Wasan tsakanin kasashen biyu shi ne na uku kuma na karshe a zagayen Twenty20 na kasa da kasa.

Kuma a ranar alhamis mai zuwa ne Ingila za ta yi karawar farko da Afghanistan a rukunin farko.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.