BBC navigation

Ingila za ta shiga gasar cin kofin duniya-Hodgson

An sabunta: 12 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 08:37 GMT
Mai horar da 'yan wasan Ingila, Roy Hodgson

Mai horar da 'yan wasan Ingila, Roy Hodgson

Mai horar da 'yan wasan Ingila, Roy Hodgson ya ce yana da kwarin gwiwar cewa tawagar kwallon kafa ta Ingila za ta kai ga gasar cin kofin duniya ta shekarar 2014 da za a yi a Brazil.

Ya bayyana hakan ne bayan an tashi kunnen doki a wasan da suka kara da Ukraine a ranar Talata.

"Na bar Wembley da kwarin gwiwa sosai game na cewa 'yan wasan da nake da su za su birnin Rio."

Ingila ta buga wasan a daren jiya ba tare da wasu 'yan wasa da suka saba buga mata kwallo ba.

Kamar su dan wasan gaba Wayne Rooney da Andy Carroll da Ashley Young da kuma Theo Walcott.

Haka kuma 'yan wasan baya John Terry da Ashley Cole ba su samu buga tamaular ba.

Abin da ya sa mai horar da 'yan wasan ya kira Raheem Sterling da Adam Lallana da Jake Livermore, wadanda ba su taba shiga tawagar Ingila a baya ba don karawa da Ukraine.

Sannan tawagar ta kuma kunshi wasu 'yan wasan da ba su da kwarewa wato Tom Cleverley da kuma Alex Oxlade-Chamberlain.

Ingila ta fara wasan cancantar shiga gasar cin kofin duniya da kafar dama, bayan ta lallasa Maldova da ci biyar ba ko daya a wasan da suka kara a ranar juma'ar da ta gabata.

Kuma karawar da kungiyar ta yi a daren jiya da Ukraine ya kara musu fatan zama tawagar da za a fafata da ita a cikin abokan karawarsu.

Sai dai tawagar ta Hodgson ba ta yi wasa sosai ba kamar yadda aka gani a Chisinau.

Ko a taka ledarta da Ukraine, Igila ta taka rawar da ba yabo ba fallasa ne, inda aka tashi ci daya da daya.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.