BBC navigation

Mai tsaron gidan Arsenal ba zai yi wasan farko ba

An sabunta: 17 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 17:10 GMT

'Yan wasan Arsenal

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal zata rasa amfani da mai tsaron gidan ta Wojciech Szczesny a wasan fara gasar cin kofin Champions League da za su kara da Kulab din Fransa Montpellier.

Dan wasan nan dan kasar Rasha, Andrey Arshavin ba a zabe shi ba zuwa tafiyar gasar.

Kochiyan kulab din Arsene Wenger zai kalli wasan ne a wajan 'yan kallo inda yake fuskantar hukuncin hana shi jagorancin wasanni uku bayan da ya tunkari Alkalin wasa a wasan su da AC Milan wanda aka yi nasara a kan su a watan Maris.

Dan gaban nan Olivier Giroud wanda ya koma Arsenal din wannan kakar wasannin yana daga cikin wadanda zasu buga wasan da tsohon kulab din sa.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.