BBC navigation

Demba Ba bai gane rawar da zai taka a Newcastle ba

An sabunta: 18 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 13:44 GMT
Demba Ba

Demba Ba

Wakilin dan wasan kwallon kafa Demba Ba, ya ce dan wasan bai fahimci rawar da zai taka a kulob dinsa na Newcastle ba, bayan wasan da aka tashi kunnen doki da Everton.

Dan wasan dan kasar Senegal mai shekaru 27 ne ya zurawa Newcastle kwallaye biyun da ta ci a ragar Everton.

Bayan kammala wasan ne kuma, Demba ya ce bai ji dadi ba da mai horar da 'yan wasan kulob dinsa, Alan Pardew bai sa shi cikin wasa tun da farko ba.

Wakilin dan wasan Alex Gontran ya ce " Tunda Demba ya dawo daga gasar zakarun kwallon kafa ta Afrika, bai fahimci alkiblar da masu kula da kulob ke fuskanta game da shi ba.

Inda ya kara da cewa " Idan har za a cigaba da sauya shi da wasu 'yan wasa ne, bayan an fara wasa to za mu duba wani zabin da muke da su."

Bayan Pardew ya ce Demba zai zauna a benchi, dan uwansa Hamady ya rubuta a shafin intanate na Twitter cewa Pardew 'Ba shi da hankali' da bai sanya Demba cikin masu taka leda ba.

Wakilin dan wasan ya kara da cewa " Demba zai so a fara kowanne gasa tare da shi, amma kuma zai mutunta shawarar da mai horar da 'yan wasan ya dauka, koda kuwa ba ta yi masa dadi ba.

Bayan kammala taka ledar dai Pardew ya kare kansa da cewa, ba zai iya farantawa kowanne dan wasa rai ba, "Amma wasu 'yan wasan ma sun fi taka leda sosai idan ransu na bace."

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.