BBC navigation

An fitar da Pietersen daga tawagar Ingila ta Kurket

An sabunta: 18 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 12:56 GMT
Kevin Pietersen

Kevin Pietersen

An fitar da Kevin Pietersen daga tawagar Ingila ta Kurket da zata je India a lokacin sanyi, duk da tattaunawar da dan wasan ya yi da masu sa ido a kan tawagar.

An cire dan wasan ne mai shekaru 32 daga tawagar a watan jiya, bayan ya aika sakonni na tsokana ta wayar salula ga 'yan wasan Afrika ta Kudu.

Sai dai an sanya wasu 'yan wasa cikin tawagar ta Ingila da suka kunshi, Joe Root da Nick Compton da Monty Panesar da kuma Samit Patel.

Pietersen yace bai ji dadin cire shi da aka yi ba.

An dai kwashe makwanni biyu ana tattaunawa, inda har kungiyar kwararru ta wasan kurket ta sanya baki, kodayake an dan samu fahimtar juna, amma hakan bai kaiga maido da Pietersen cikin tawagar a wannan matakin ba.

Babban daraktan hukumar dake sa ido a kan 'yan wasan na Ingila, Hugh Morris ya ce " Har yanzu akwai batutuwan da ba a kai ga warware su ba, shi yasa ba a zabi Kevin cikin tawagar da za ta tafi India ba."

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.