BBC navigation

Chelsea za ta kara da Juventus

An sabunta: 19 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 17:00 GMT

Shugabannin Duniya na kallon Champions League

A yau ma dai ana ci gaba da gasar Champions League inda a halin yanzu ake wasanni takwas. Sai dai wasannin da suka fi jan hankali sune na Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea da take gwabzawa da Juventus da kuma Manchester united take karawa da Galatasaray.

Sauran wasannnin da ake yi sun hada da Barcelona da Spartak Moscow, Bayern Munich kuma na karawa da Valencia, haka kuma Celtic na karan batta da Benfica.

Lille kuwa za ta fafata ne da Bate Borisov, Shakhtar Donetsk kuwa da Nordsjaelland.

A jiya ma dai anyi wasanni takwas inda wasan Real Madrid da Manchester City akayi gumurzu daga karshe Real Madrid ta samu nasara kan Manchester city da ci uku da biyu duk kuwa da cewa Manchester City ce ta fara zura kwallo a ragar Real Madrid.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.