BBC navigation

Manchester United na tare da Liverpool - Ferguson

An sabunta: 19 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 11:47 GMT
Sir Alex Ferguson

Sir Alex Ferguson

Mai horar da 'yan wasan kulob din Manchester United, Sir Alex Ferguson ya ce kulob din zai taimakawa Liverpool ta kowace hanya.

Ya fadi hakan ne a wata ganawa da kulob din biyu suka yi a ranar lahadi, mako daya bayan fitar da rahoton nan game da bala'in nan na Hillsborough.

Man U ta soki magoya bayanta da suka shiga cikin masu tsokanar 'yan Liverpool a taka ledar da kulob din ya yi da Wigan.

Masoya wasan kwallon dai sun yi ta rera wakar tsokana a filin wasa na Old Trafford, inda aka yi wasan.

Ferguson ya ce " Ni ban ji wakar da kunne na ba, amma wasu sun ji, wannan wata tsokana ce da aka fara tun lokacin al'amarin nuna wariyar launin fata tsakanin Lius Suarez da kuma Patrice Avra. "

Ya kara da cewa " Sake jin wakar abin bakin ciki ne. Wasu da ba su da rinjaye ne suka yi, amma mu al'umma ne da marasa rinjaye ke son a ji muryarsu. "

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.