BBC navigation

Suarez da Evra za su gaisa kafin wasa

An sabunta: 19 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 15:53 GMT

Patrice Evra da Luis Suarez

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool da takwarar ta Manchester United suna da kwarin gwiwar cewa Luis Suarez da Patrice Evra za su gaisa kafin a fara wasan gasar Premier League a Anfield ranar Lahadi.

Hukumomin kulob din biyu sun kammala shirin tuna ranar da aka fitar da rahoton nan game da bala'in nan na Hillsborough.

Amma an dai nuna jin tsoron ko wani abu zai iya faruwa da Suarez wanda aka hana shi wasanni takwas bayan da ya nuna wariyar launin fata ga dan bayan United kakar bara, Patrice Evra, sai dai duka kulob kulob din sun karfafa bukatar kowanne dan wasa ya girmama bikin.

Kochiyan Manchester United Sir Alex Fergusson dai tuni ya nuna cewar kulab din sa zai taimakawa Liverpool ta kowace fuska.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.