BBC navigation

Mancini ya gargadi Joe Hart kan sukar 'yan wasa

An sabunta: 19 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 08:13 GMT
Mai horar da 'yan wasan Manchester City, Roberto Mancini

Mai horar da 'yan wasan Manchester City, Roberto Mancini

Mai horar da 'yan wasan kulob din Machester City, Roberto Mancini ya ja kunnen mai tsaron gida Joe Hart da ya daina sukar 'yan wasa.

Inda ya jaddada cewa shi kadai ne ya dace ya yanke hukunci.

Sau biyu kulob din na City ya sha gaban Real Madrid a gasar Champions League, amma ya sha kaye da ci uku da biyu a taka ledar da aka yi a Bernabeu.

Joe Hart yace " Bai kamata ace muna da ci biyu da daya ba, kuma mu sha kaye saura mintoci biyar a kammala wasa, laifinmu ne ba na wani ba."

Shi kuwa Mancini ya maida martani ne da cewa " Idan akwai wanda ya kamata ya soki 'yan wasa to ni ne, ba Joe Hart ba."

"Ya kamata Joe Hart ya tsaya a matsayinsa na mai tsaron gida, domin ni ya kamata in yanke hukunci." Inji Mancini.

Kulob din na City ya fuskanci matsin lamba sosai a taka ledar na Bernabeu, kafin dan wasa Edin Dzeko ya sanya kwallo na farko a ragar Real Madrid.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.