BBC navigation

Hodgson ya yi kira ga talabijin kan wasanni

An sabunta: 20 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 16:37 GMT

Roy Hodgson

Manajan Ingila Roy Hodgson ya bukaci gidajan talbajin da su dakatar da gudanar da wasanni na Premier League tsakanin manyan kulob kulob a ranakun Lahadi kafin wasanni na kasa da kasa.

Hujjar da ya bayar itace, 'yan wasan da suka samu rauni ba sa samun damar murmurewa da kuma hutawa, abin da kuma ke yin tasiri dan gane da shirye shiryen su na tunkarar wasa na gaba.

Hodgson ya furta cewa: " hutun lokacin hunturu ya yi daidai da tsarin jadawalin kakar wasa a Ingila".
Ya sake jaddada cewa : "ya yi kyau idan mu ka yi tunanin cewa, wata rana za mu zo baki daya mu ce Ingila na da muhimmanci".

Guda hudu daga cikin kungiyoyi takwas na Ingila da su ka rage zuwa halartar wasannin cin kofin duniya za su fafata a ranar Juma'a.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.